Saurari premier Radio
40.5 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBa yakin neman zabe ya kawoni Kano ba-Tinubu

Ba yakin neman zabe ya kawoni Kano ba-Tinubu

Date:

Dan takarar shugaban kasa a jami’iyyar APC Bola Ahamd Tinubu ya ce wasu al’amuran siyasa ne suka kawo shi Kano ba yakin neman zabe ba.

 

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi wajen bude ofishin jami’iyyar APC na Kano ranar Asabar.

 

A don hakanne ya kirayi jama’a da suyi watsi da kalaman da wasu ke yadawa cewa shugaban kasa bai yi katabus ba wajen yakin neman zabensa a Kano.

 

*Ba kamfe ne ya kawoni Kano ba, wasu dalilai ne na siyasa, don na gana da wasu muhimman mutane na jihar, sannan na bude ofishin jam’iyya.

 

“Idan lokaci ya yi na yakin neman zaben zamu dawo Kano don neman goyon bayan al’ummar jihar, don jihar ta APC ce” A cewarsa.

 

Tinubu ya kuma yaba da kokarin da mata ke yi, inda ya bukacesu da su kara himma kan wanda suke da shi.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...