Yara sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ba da fifiko wajen amincewa da dokar kare hakkin yara a matsayin dokar kasa.
Sun yi wannan kiran ne a ranar Juma’a a Abuja yayin wani taron manema labarai da kungiyar Save the Children International, Najeriya ta shirya, domin tunawa da ranar yara mata ta duniya ta bana.
A halin da ake ciki dokar da aka zartar a shekara ta 2003 za ta iya yin tasiri ne kawai idan Majalisar Dokokin Jihohi suka tsara suka kuma amince da dokar.
Maryam Ahmed, Jakadiyar Matasa ta Save the Children, ta ce duk da cewa an kafa dokar kare hakkin yara a jihohi 31 ya zuwa yanzu, ba duka jihohin ne ke aiwatar da dokar yadda ya kamata ba.