24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiNoman rogo ya samarwa miliyoyin yan Najeriya aikin yi - Masana

Noman rogo ya samarwa miliyoyin yan Najeriya aikin yi – Masana

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Daga Hafsat Iliyasu Dambo

 

Kididdgar da masana amfanin gona suka fitar ta tabbatar da noman Rogon ya taimaka wajen samar wa da miliyoyin ‘yan Nijeriya aikin yi.

Masanan sun bayyana cewa, daga cikin tan miliyan 53 na rogon da ake noma wa a Nijeriya a duk shekara, fiye da kashi 90 cikin dari ana sarrafa shi zuwa sauran nau’ikan abinci.

Masana sun kara da cewar matukar aka inganta fannin, zai samar da fiye da hakan.

A cewar masanan, Nijeriya ce ke kan gaba wajen noman rogo, inda suka bayyana cewa, kasar ta samar da kimanin tan miliyan 53 na rogo a shekarar 2018.

Hakazalika, Kasar ta na samar da akalla tan 7.7 ako wacce kadada daya, idan aka kwatanta da tan 23.4 da kuma tan 22.2 da ake samarwa a kasashen Indonesiya da Thailand.

Masanan sun tabbatar da cewa,matukar gwamnati ta maida hankali wajen inganta noman rogo a fadin kasar nan ta hanyar fitar da shi zuwa kasuwar duniya zai kara samarwa kasar kudaden shiga masu dimbin yawa.

Latest stories