33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiSarkin Zazzau ya ce tsananin fari na fuskanto Arewa

Sarkin Zazzau ya ce tsananin fari na fuskanto Arewa

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Daga Hafsat Iliyasu Dambo

Sarkin Zazzau Ahmed Nuhu Bamali ya gargadi shugabannin Arewa da su tashi tsaye domin tunkarar matsalar yunwa mai tsananin dake yiwa kasar barazana.

 

Sarkin yace ambaliyar ruwan da ya addabi sassan arewacin kasar nan tare da ayyukan ‘yan bindigar da suka hana noma a yankin sune mujazar wannan matsalar.

 

Ahmed Nuhu Bamali yace mutanen yankin basa bukatar wani masanin da zai shaida musu cewar an kama hanyar karancin abincin da kuma yunwa sakamakon wadannan matsaloli guda biyu da suka hana jama’a gudanar da harkokin su na noma wanda shine babban sana’ar da aka sansu da shi.

 

Sarkin yace duk da yake suna ci gaba da addu’a domin Allah ya kawowa jama’a dauki, ya zama wajibi a fadakar da mutane da su tashi tsaye domin samun madogara saboda ganin girmar matsalar.

 

Basaraken yace lokaci yayi da jama’ar yankin zasu tashi daga baccin da suke yi domin sake dabaru ganin yadda a shekaru 2 da suka gabata, yankin yayi fama da wadanan tagwayen matsaloli a jere.

Latest stories