Tsagin ADC ƙarƙashin jagorancin Nafiu Bala ya buƙaci bangaren da David Mark ke jagoranta da ya dakatar da sayar da fom ɗin neman tsayawa takara har sai an kammala shari’ar da ke gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Lamarin na zuwa ne yayin da babbar kotun tarayya ta ɗage shari’ar shugabancin jam’iyyar da Nafiu Bala ya shigar ba tare da sanya wata sabuwar rana ba.
sakataren kwamitin amintattu na ADC, Rufus Akanmi ne ya fitar da sanarwar gargadin a Abuja ranar Juma’a, 8 ga Mayu, 2026.
Tsagin Nafiu Bala ya ce buƙatar dakatar da sayar da fom ɗin na cikin matsayar da aka cimma a taron kwamitin amintattun jam’iyyar da aka gudanar ranar Alhamis.
Ya yi gargaɗin cewa duk wanda ya ci gaba da sayen fom ɗin takara bayan wannan umarni da ya bayar to ya yi kuka da kan shi.
Tsagin Nafiu Bala ya kuma yaba wa kotun koli bisa hukuncin da ta yanke ranar 30 ga Afirilu, 2026, inda ya bayyana hukuncin a matsayin wata babbar gudunmawa ga dimokuraɗiyya, kundin tsarin mulki da bin doka a tsarin siyasar Najeriya.
