Kasashen Najeriya da Amurka sun kulla yarjejeniyar kara zurfafa hadin gwiwa a fannin tsaro, domin yaki da ta’addanci da tabbatar da zaman lafiya a yankin Yammacin Afirka.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai taimakawa Shugaba Tinubu kan yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar.
Sanarwar ta ce kulla yarjejeniyar ta biyo bayan ziyarar aiki ta kwanaki uku da mai bawa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu Shawara kan tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, ya kai Amurka, inda ya gana da manyan kusoshin gwamnatin kasar.
Yayin ziyarar, Ribadu ya gana da Mataimakin Shugaban Amurka, J.D. Vance, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio da Sauran manyan jami’an diflomasiyya da na tsaron kasar, inda ya isar da sakon Shugaba Tinubu na kara jajircewar Najeriya wajen dorewar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Sanarwar ta ce babban makasudin ganawar shi ne domin a duba yadda za’a inganta musayar bayanan sirri da karfafa ayyukan soji na hadin gwiwa, da jaddada muhimmancin taimakon juna don magance matsalolin tsaro da suka addabi yankin Sahel, Safarar miyagun kwayoyi da makamai da Laifukan da ake aikatawa ta hanyar yanar gizo.
Hukumomin Amurka sun jinjinawa Najeriya a matsayinta na jagora a yankin Afirka, musamman wajen jagorantar yaki da ta’addanci a tafkin Chadi.
A karshen taron, bangarorin biyu sun amince su ci gaba da tuntubar juna akai-akai ta hanyar hadin gwiwa na musamman don tabbatar da cewa dukkan yarjejeniyoyin da aka kulla sun fara aiki yadda ya kamata.
