Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan, ya bukaci matasan Najeriya su shiga harkokin zabe gadan-gadan yayin da ake tunkarar babban zaben shekarar 2027.
Jonathan ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Alhamis lokacin da wasu matasa suka kai masa ziyara a gidansa domin rokon sa ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2027.
Da yake jawabi ga matasan, tsohon shugaban kasar ya bukace su da su mallaki katin zabe na dindindin, wato PVC, tare da shiga harkokin zabe yadda ya kamata.
Ya kuma bukaci hukumar zabe ta kasa INEC ta duba matsalar rashin sha’awar zabe da ke kara yaduwa a Najeriya, yana mai cewa mutane da dama ba sa nuna sha’awa wajen kada kuri’a.
Jonathan ya ce wajibi ne matasa su kasance cikin tsarin zabe da harkokin dimokuradiyya.
Ya ce, “Mai yiwuwa rabin ku ba su da katin zabe, amma kuna son in tsaya takara.”
Tsohon shugaban ya zama shugaban kasa ne a ranar 5 ga Mayun 2010 bayan rasuwar tsohon Shugaba Umaru Musa Yar’Adua.
Daga baya kuma, an sake rantsar da shi a ranar 29 ga Mayun 2011 bayan nasararsa a zaben shugaban kasa na shekarar 2011.
Ko da yake Jonathan bai bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a 2027 ba, wasu yan Najeriya na ci gaba da kira gare shi da ya dawo takara.
