Aminu Abdullahi Ibrahim
Hukumar ilimin bai daya (SUBEB) ta mika takardu daukar aiki ga sakatarorin ilimi na kananan hukumomin Kano domin raba su ga sabbin malaman da gwamnan Kano ya dauka.
An gudanar da rabon takardun ne a shalkwatar hukumar dake sakatariyar Audu Bako ranar Alhamis.
Yayin rabon takardun shugaban hukumar (SUBEB) Yusuf Kabir da ya samu wakilcin kwamishina na 1 a hukumar Wada Ibrahim Daho, ya ce gwamnan Kano ya amince a biya sabbin ma’aikatan albashi daga watan Yuli duba da wahalhalul da suka sha.
Ya ce a cikin sabon shirin an dauki malamai dubu 4,900 yayin da aka dauki ‘yan Besda dubu 3,688.
Ya ce cikin kwanaki 4 sakatarorin ilimi zasu baiwa kowane malami takardar shaidar daukar aikinsa.
Gwamnan Kano ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da baiwa ilimi, da horas da matasa sana’a fifiko
Wada Ibrahim Daho, ya bukaci sabbin ma’aikatan su mayar da hankali akan aikin su don tabbatar da cigaban ilimi.
A nasa bangaren sakataren Ilimi na karamar hukumar birni da yayi jawabi amadadin sakatarorin ilimi na kananan hukumomin Kano 44 kwamaret Nura Sulaiman ya ce zasu sanya ido don tabbatar da cewa kowane malami yana gudanar da aikinsa yadda ya kamata.
Ya nuna godiyarsa bisa yadda gwamnan Kano ya zabi a basu takardun domin mika su ga sabbin malaman.
