Gwamnan wamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ce duk faɗin Najeriya babu wani titin gadar sama ko na gadar ƙasa da ya kai kyau da tsaruwar gadar ƙofar Ɗan agundi, la’akari da yadda ƙwararru suka zuba tarin ilimin su wajen samar da ita.
Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da yake baiwa matasan dake gudanar da sana’o’i da tallace-tallace akan tituna da danjojin tsayawar mota a Kano su 1,116 tallafin naira dubu 50 kowannen su.
Gwamna Abba ya ce baiwa matasan tallafin kuɗin da yawan su ya zarce naira miliyan 55 lokaci guda, zai taimaka musu wajen bunƙasa sana’o’in da suke yi akan tituna da danjojin motoci a Kano tare da ɗauke hankalin su daga aikata munanan laifuka.
Gwamna ya kuma sha alwashin ci gaba da tallafawa masu ƙananan sana’o’i a faɗin Kano da nufin sauya tunanin matasa maza da mata a jihar daga abubuwan da basu da amfani ya zuwa yadda zasu taimakawa kan su da al’ummar su.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa Wasu daga cikin matasan da aka tallafawa sun jinjinawa yunƙurin na gwamna Abba, inda suka bashi tabbacin cewar zasu yi amfani da tallafin ta kyakkyawar hanyar musamman wadda za ta haɓaka tattalin arzikin Kano.
