Shugabannin ’yan kasuwa daga manyan kasuwanni 25 na Kano sun bayyana goyon bayansu ga Gwamna Abba Kabir Yusuf, tare da amincewa ya sake tsayawa takarar gwamna a wa’adin mulki na biyu a zaɓen 2027.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar.
’Yan kasuwar sun bayyana matsayar tasu ne, yayin wata liyafar cin abinci da aka gudanar a Gidan Gwamnatin Kano.
Ƙungiyar, ƙarƙashin jagorancin dattijo kuma fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Sabi’u Bako, ta ce za ta marawa Gwamna Yusuf baya a ƙarƙashin jam’iyyar APC.
‘yan kasuwar Sun ce sun ɗauki wannan mataki ne saboda manufofi da shirye-shiryen gwamnatin, musamman waɗanda suka shafi inganta harkokin kasuwanci, gyaran kasuwanni, samar da hanyoyin shiga kasuwanni da hasken rana, da kuma sauƙaƙa harkokin kasuwanci.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito ‘yan kasuwar na cewa ayyukan farfaɗo da birane da sauye-sauyen tsarin karɓar haraji na daga cikin abubuwan da suka ƙara musu kwarin gwiwa wajen mara wa Gwamnan baya, tare da tabbatar da ci gaba da ba gwamnatin haɗin kai wajen ci gaban Kano.
