Wata kotu ta musamman da ke sauraron shari’o’in satar mutane da ayyukan asiri a jihar Edo ta yanke wa mutum huɗu, ciki har da wata mata mai shekaru 27, hukuncin kisa ta hanyar rataya ko allurar kashewa, bayan samunsu da laifuffukan da suka haɗa da garkuwa da mutane da fashi da makami.
Waɗanda aka yanke wa hukuncin sun haɗa da Marvelous Isaac mai shekaru 32, Wisdom Michael mai shekaru 36, Rufus Emete Michael mai shekaru 30, da Gift Raphael mai shekaru 27, mai shari’a Aigbona Terry Momodu ne ya yanke hukuncin a ranar Talata, bayan sauraron shari’ar da ta ƙunshi tuhume-tuhume 11.
Shari’ar ta samo asali ne daga sace wata mata da wasu ’yan bindiga suka yi a ranar 14 ga Yuni, 2026, a kasuwar kayan lambu da ke kan titin airport road a birnin Benin, babban birnin jihar Edo, rahotanni sun ce an sace matar ne da rana tsaka, yayin da take tare da mijinta da ’ya’yanta.
A yayin shari’ar, masu gabatar da ƙara sun gabatar da shaidu bakwai da kuma wasu muhimman bayanai, ciki har da hotunan kyamarorin CCTV da suka taimaka wajen danganta waɗanda ake tuhuma da laifin, alkalin ya bayyana cewa masu gabatar da ƙara sun tabbatar da zarge-zargen da ake yiwa waɗanda ake tuhuma ba tare da barin wani ƙwaƙƙwaran shakku ba.
Sai dai lauyan Gift Raphael, Felix Imasuen, ya bayyana cewa za su ɗaukaka ƙara kan hukuncin, a nasa ɓangaren, babban lauyan gwamnatin jihar Edo, Roland Otaru, ya yaba wa kotun bisa hukuncin, yana mai cewa zai zama izina ga masu aikata laifuffuka.
Hukuncin ya zo ne a yayin da jihar Edo ke ƙoƙarin hanzarta shari’o’in da suka shafi garkuwa da mutane da ayyukan asiri, ta hanyar kafa kotuna na musamman domin sauraron irin waɗannan laifuffuka.
