Gwamnatin Kano ta ce za ta dauki tsatstsauran matakin shari’a, kan duk gurɓataccen ɗan kasuwar da ta kama yana sauya adadin wutar batir ko Panel ɗin Solar, domin ya siyar a farashi mai tsada ga al’umma.
Shugaban hukumar kare hakkin mai saye da sayarwa ta jihar Dr Ibrahim Garba Muhammad ne ya bayyana hakan lokacin da ƙwararru a hukumar suke gwada batira da panel din solar da suka kama a kasuwannin jihar.
Dr Garba ya ce matakin ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da hukumar take yawan karɓa daga al’ummar Kano masu sayan kayan Solar a kasuwannin jihar ke ci gaba da yi kan yadda wasu ‘yan kasuwa ke yaudarar kwastomomi ta hanyar sauya bayanan kayayyakin domin su nuna suna da ƙarfin da ba su da shi.
Dr Ibrahim Garba ya jaddada cewa gwamnati ba za ta lamunci duk wani nau’in damfara ko cutar da masu sayen kayayyaki a jihar ba, tare da tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa Dr Garba ya kuma buƙaci al’umma da su dinga sayen kayayyakin hasken rana daga amintattun dillalai tare da kai rahoton duk wani zargin magudi ga hukumar domin ɗaukar matakin da ya dace.
