Jam’iyyar (NDC) ta ce hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja ba zai hana ta ci gaba da shirye-shiryen zaɓen 2027 ba, duk da sabon umarnin kotu.
Jam’iyyar ta ce tun bayan rajistarta, ta ci gaba da gudanar da ayyukanta a fadin ƙasar nan ciki har da rajistar mambobi, tarurrukan jam’iyya da kuma zaɓen fidda gwani.
NDC ta kuma ce ta shiga wasu zaɓukan cike gurbi tare da tsayar da ‘yan takara a matakai daban-daban na zaɓen 2027 da ke tafe.
Sai dai jam’iyyar ta bayyana rashin amincewa da hukuncin kotun, tana mai cewa za ta ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara domin kalubalantar matakin.
Jam’iyyar ta kuma tabbatar wa mambobinta cewa duk shirye-shiryenta na siyasa suna nan daram, tare da kira a ci gaba da mara mata baya yayin da take neman samun adalci a kotu.
