Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci ƙaddamar da shirin sayar da buhunan takin zamani guda dubu 90,000, wanda gwamnatin sa ta yi ragin kashi 50 cikin 100 akan kowane buhu, domin tallafawa manoma a ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Da yake kaddamar da shirin, Gwamna Abba ya bayyana cewa shirin wani ɓangare ne na ƙudirin gwamnatinsa na bunƙasa harkar noma, ƙarfafa samar da abinci da kuma ragewa manoma tsadar kayan aikin noma.
Gwamna Abba ya ce gwamnatin jihar ta ɗauki matakin bayar da ragin kashi 50 cikin 100 ne domin tabbatar da cewa ƙananan manoma sun samu takin cikin sauƙi, musamman a daidai lokacin da damuna ke ƙara kankama.
Gwamna Abba ya ce kowace karamar hukuma zata samu tirela 3 ta takin, wanda yawan sa ya kama dubu 1 da dari takwas, inda mutune 70 zasu amfana da tsarin a kowace mazaɓa dake fadin jihar Kano.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamnan na jaddada cewa an tsara yin rabon takin ne cikin gaskiya da adalci domin tabbatar da cewa waɗanda suka cancanta ne kawai za su amfana da shirin a dukkan ƙananan hukumomin jihar.
