Gwamnatin Kano ta ce akwai bukatar malamai, Masarautu, ‘yan siyasa, masu ruwa da tsaki da masu fada aji a matakin kasa, su yi kwakwayon kasashen duniya wajen samar da dokar hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da safarar miyagun kwayoyi zuwa Najeriya.
Shugaban hukumar samar da magunguna da kayan aikin asibiti ga asibitoci mallakin gwamnatin Kano Pharmacist Ghali Sule ne ya bayyana hakan a wajen taron da Kungiyar samar da zaman lafiya da ci gaban ilimi ta shirya domin lalubo hanyoyin dakile bazuwa da tu’ammali da miyagun kwayoyi.
Pharmacist Ghali ya ce dukkan kasashen da suka rungumi dokar kisa ga masu shigar musu day miyagun kwayoyi sun samu gagarumar nasara wajen dakile shigar musu da su,a dan haka lokaci yayi da ya kamata Najeriya ma ta rungumi tsarin matukar ana san kawo karshen matsalar.
Da yake bayyana makasudin shirya taron, shugaban kungiyar ta samar da zaman lafiya da ci gaban ilimi reshen Kano Auwal Abdullahi Yola ya ce matukar ana fatan kawo karshen matsalar miyagun kwayoyin a Kano da Najeriya, dole sai kowa ya bada gudunmawa mahukunta kuma su dauki matakan ba sani ba Sabo.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya a rawaito cewa taron an gudanar da shi ne a dakin taro na makarantar koyar da harshen larabci ta SAS inda ya samu halartar manyan baki daya ciki da wajen Kano.
