Wani ƙwararren likitan a jihar Kano ya rasu mintuna 15 kacal bayan ya isa Asibitin Arewa Surgery da ke Hotoro domin duba marasa lafiyar da suka shafe sa’o’i suna jiransa.
Lamarin ya faru ne a ranar Asabar da ta gabata, bayan an nemi marigayin, Dr. Ibrahim, ya maye gurbin wani likita da ba zai samu damar zuwa duba marasa lafiyarsa ba.
Wani mataimaki ga gwamnan jihar Jigawa, Suleiman Harbo, wanda ya je asibitin tare da mahaifiyarsa domin ganin likita, shi ne ya bayyana yadda lamarin ya faru.
Harbo ya ce sun isa asibitin da misalin ƙarfe 5:00 na yamma, inda aka sanar da su cewa likitan da aka tsara zai duba marasa lafiya ba zai samu damar zuwa ba, saboda haka aka tuntuɓi Dr. Ibrahim.
Ya ce marasa lafiya kusan shida, mafi yawansu sun haura shekara 80 da haihuwa, suna jiran isowar likitan.
Bayan ya tambayi dalilin jinkirin, ma’aikatan karɓar baƙi sun kira Dr. Ibrahim ta waya, suka sanar da shi cewa tsofaffin marasa lafiya na jiransa.
A cewarsa, Dr. Ibrahim ya ce zai zo bayan ya idar da sallar Magariba.
Da isowarsa asibitin, rahotanni sun ce nan take bayan ya fito daga motarsa ya fara jin jiri, inda aka garzaya da shi sashen gaggawa.
Sai dai duk da ƙoƙarin da wasu manyan likitoci suka yi na ceto rayuwarsa, an tabbatar da rasuwarsa cikin mintuna 15.
Harbo ya ce lamarin ya girgiza marasa lafiya da ma’aikatan asibitin.
Ya ƙara da cewa abin tausayi shi ne duk marasa lafiyar da ke jiran ganin likitan sun haura shekaru 80, amma duk da ƙoƙarin da kusan manyan likitoci biyar suka yi wajen ceton rayuwarsa, sun kasa.
Ya ce mahaifiyarsa ba ta san abin da ya faru ba da farko, sai da ta tambaye shi ko likitan ya iso. Kafin ya ba ta amsa, wani mara lafiya ya sanar da ita cewa likitan da suke jira ya rasu.
Da jin haka, ta ce: “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Ashe shi ne likitan da aka garzaya da shi ciki? Allah Ya jikansa. Mu tafi gida, ni ma na samu lafiya.”
Harbo ya ce ya kasa riƙe hawaye yayin da yake mayar da mahaifiyarsa gida.
Ya kuma bayyana cewa mutanen da suke tare da Dr. Ibrahim a lokacin ƙarshe sun ce kalamansa na ƙarshe su ne:
“La ilaha illallah.”
Har yanzu ba a bayyana musabbabin faɗuwar da ta yi sanadin rasuwar Dr. Ibrahim ba. Allah Ya jikansa da rahama.
