Hukumar NDLEA a Kaduna ta kama mutane 1,107 tare da kwace sama da kilo dubu 12 na miyagun ƙwayoyi tsakanin watan Yunin 2025 zuwa Yunin 2026.
Kwamandan hukumar a jihar, CN Maijama’a Muhammad, ya ce an kama hodar iblis, tabar wiwi, tramadol da sauran ƙwayoyi masu sa maye, yayin bikin Ranar Yaƙi da Shan Miyagun Ƙwayoyi ta Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ya ce an gurfanar da mutane 284 a kotu, inda 245 daga cikinsu aka same su da laifi, yayin da mutane 94 suka kammala gyaran hali, kuma 78 suka kamala jinya cikin nasara.
Hukumar ta kuma rusa wuraren sayar da miyagun ƙwayoyi 662 a faɗin jihar, tare da ba mutane 1,458 shawarwari da tallafin daina shaye-shaye.
Kwamandan ya yi kira ga iyaye, makarantu, shugabannin al’umma da hukumomi su haɗa kai wajen yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi domin gina al’umma mai zaman lafiya.
