Gwamnatin tarayya ta ce za ta ci gaba da yaƙi da rashin aikin yi, rage talauci da kuma daƙile bara da tumasanci ta hanyar zuba jari a fannin koyar da sana’o’i da ƙwarewar fasahar zamani da horar da mata da matasan kasar da tallafa musu da kayan aiki.
Mataimakin Shugaban kasa Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a Kano, yayin da Hukumar Kula da Kimiyya da Kere-kere ta kasa NASENI, ta kaddamar da shirin koyawa mata da matasa sana’o’in dogaro da kai da basu kayan aikin sana’ar da aka koya musu.
Sanata Kashim Shettima, wanda mai taimaka masa nu musamman Musaddiq Mustafa Adamu ya wakilta ya yabawa NASENI bisa gudunmawar da take bayarwa wajen tallafawa ƙoƙarin Gwamnatin tarayya na ƙarfafawa ‘yan Najeriya gwiwa ta hanyar kirkire-kirkire da koyar da sana’o’i.
Tun da farko, Shugaban Hukumar ta NASENI, Malam Khalil Suleiman Halilu, ya ce haɗin gwiwar da ke tsakanin hukumar da gwamnatin jihar Kano wajen koyar da maza da mata sana’o’in zamani zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi, rage talauci da kuma yaƙi da bara.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito gwamnan Kano Abba Kabir Yusif wanda ya samu wakilcin kwamishinan kudi na jihar Dr Isma’il Aliyu Dan maraya na bayyana shirin a matsayin wanda ya zo akan lokaci, tare da yabawa NASENI bisa ƙoƙarinta na inganta rayuwar mata da matasa ta hanyar koyar da su sana’o’i da ba su damar dogaro da kai.
