Shugaban kasar Bola Ahmad Tinubu zai kai ziyarar aiki zuwa ƙasashe uku a jere, inda zai ziyarci ƙasashen Faransa da Kenya da kuma Rwanda.
Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Bayo Onanuga ya fitar, inda ya ce shugaban zai bar Najeriya a yau Asabar 2 ga watan Mayu.
Sanarwar ta kara da cewa, shugaban kasa Tinubu zai fara sauka a Faransa daga nan zai wuce Nairobi babban birnin kasar Kenya, inda zai halarci taron haɗakar ƙasashen Faransa da kuma Afirka wanda Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Kenya William Ruto za su jagoranta.
Ya ce za a gudanar da taron ne domin samar da hanyoyin inganta kasuwancin zamani da makamashi da sauyin yanayi da kuma sauran abubuwa masu muhimmanci.
Bayo Onanuga ya kara da cewa, bayan taron shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu zai tafi ƙasar Rwanda, domin halartar taron manyan shugabannin kamfanoni na Afirka wanda za a yi a ranakun 14 da 15 ga watan Mayu, inda a cewarsa daga kasar ta Rwanda ne shugaban kasar zai dawo Najeriya.
