An samu sauyi a shugabancin kungiyar Takai Local Government Progressive Youths Initiatives bayan gudanar da wani taro ta manhajar WhatsApp, inda aka tattauna kan bukatar da wasu mambobi suka gabatar na saukar tsohon shugabanta Umar Sabo Algamawy bisa zargin kaucewa tsarin manufofin kungiyar.
Bayan kammala taron, ta tabbata cewar mambobin sunce ba zai yiwu kungiyar ta ci gaba da aiki ba tare da shugabanci ba, lamarin da ya sa aka cimma matsaya kan samar da sabon shugabanci na rikon kwarya domin tafiyar da harkokin kungiyar.
Bisa wannan matsaya, an nada tsohon sakataren kungiyar, Badamasi Ibrahim Galadima, a matsayin shugaban rikon kwarya, yayin da Najib Isyaku Ali, wanda shi ne tsohon Financial Secretary, ya zama sakataren rikon kwarya. Haka kuma, Ahmad Hamza (Tijjani) ya karbi mukamin Financial Secretary.
Sabon shugaban rikon kwarya ya bukaci mambobin kungiyar da su hada kai, su mayar da hankali kan manufofin kungiyar, tare da nuna jajircewa da hakuri domin ciyar da kungiyar gaba.
