Yayin da sauyin fasahar zamani ke ci gaba da sauya tsarin tattalin arziki a faɗin duniya, masanin ilimin na’ura a Birnin Maiduguri Jihar Borno, Abdulrahman Ali, wanda aka fi sani da Abban Farida, na taka muhimmiyar rawa wajen samarwa matasan Nijeriya ilimin zamani domin bunƙasa ci gaba ta hanyar ilimin fasaha.
Abban Farida, mamallakin kamfanin Masfo Global Connect Ltd, na aiki ne a fannoni daban-daban na ilimin fasahar zamani da suka haɗa da ilimin kwaikwayon basirar danAdam (AI), fasahar blockchain, da ilimin dijital baki daya. Manufarsa ita ce, samar da ilimin zamani ga matasa domin damawa da su a duniya musamman ga waɗanda ke zaune a yankunan da ke fama da ƙarancin ilimin fasahar zamani.
Masfo Global Connect Ltd dake da shafin www.masfoglobal.com na ƙara samun ɗaukaka a cikin tsarin fasaha a Nijeriya ta hanyar gudanar da shirye-shiryen horo da ƙarfafa matasa a fannin dijital domin ba su ƙwarewa a harkokin shirye-shiryen kwamfuta, Web3, da kasuwancin yanar gizo.
Masana harkar fasaha sun bayyana cewa shirye-shirye irin na kamfanin Masfo Global Connect na nuna yadda ƙirƙire-ƙirƙire daga matakin ƙasa ke ƙaruwa a Arewacin Nijeriya, inda a baya damar samun kayayyakin dijital da irin waɗannan damammaki suka kasance ƙalilan.
Da yake magana kan hangen nesan kamfanin, Abdulrahman Ali ya jaddada muhimmancin bai wa kowa dama a tsarin samun tattalin arzikin dijital.
Kamfanin ba ga harkokin dijital kadai ya tsaya ba, har ma da binciken damammaki a fannin noma mai ɗorewa da kasuwancin dijital tsakanin ƙasashe, daidai da tsarin duniya kan dorewar tattalin arziki da bunƙasa hanyoyin samun kuɗaɗe daban-daban.
