Saurari premier Radio
24.9 C
Kano
Wednesday, May 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiTinubu, ya sa hannu kan dokar bai wa ɗalibai bashin kudin karatu.

Tinubu, ya sa hannu kan dokar bai wa ɗalibai bashin kudin karatu.

Date:

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya sa hannu kan dokar bai wa ɗalibai bashin kudin karatu.

Tinubu ya sa hannu kan dokar ce a fadarsa da ke Abuja.

Dokar mai taken kudurin sauya wa dokar bai wa dalibai rancen kudin karatu fasali ta 2024, an samar da ita ne domin kafa asusun tallafa wa daliban makarantun gaba da sakandire.

A watan Nuwambar shekarar da ta gabata ne majalisun tarayya suka amince da kudurin dokar, da ke neman kafa wata gidanauniyar da za ta rika bai wa daliban manyan makarantun kasar nan bashin kudin makaranta.

Sabuwar dokar dai ita ce irinta ta farko a kasar nan, kuma a karin bayanin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, wanda shi ne ya kawo kudurin dokar lokacin yana kakakin majalisa, za ta inganta bangaren ilmi, saboda a cewarsa daga yanzu babu yaron da zai gaza samun damar yin karatu a marantun gaba da sakandire saboda matsalar rashin kudin makaranta.

Latest stories

Related stories