Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya karɓi Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar na III, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, ranar Alhamis.
Ganawar ta gudana ne a fadar shugaban ƙasa, inda ake sa ran tattauna muhimman batutuwan da suka shafi zaman lafiya da haɗin kan al’ummar Najeriya.
A cewar rahoton jaridar Daily Trust, Sarkin Musulmin ya yi kira da a gudanar da yakin neman zaɓen 2027 cikin lumana, tare da jan hankalin ’yan siyasa da magoya bayansu da su guji kalaman tunzura jama’a da duk wani abu da zai iya haddasa tashin hankali.
Ya jaddada muhimmancin zaman lafiya da mutunta juna wajen tabbatar da sahihin tsarin dimokuraɗiyya a Najeriya.
