Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA), reshen Jihar Kano, ta yi kira ga al’umma da su guji sayar da ƙuri’unsu da kuma shiga rikicin siyasa gabanin babban zaɓen 2027.
Daraktan hukumar na ƙasa, Malam Lanre Isa Onilu, ya bayyana hakan ta bakin wakilinsa, Barista Williams Manya Dogo, yayin ziyarar wayar da kan jama’a a fadar Sarkin Rano.
Ya ce hukumar na gudanar da gangamin ne domin faɗakar da al’umma kan muhimmancin zaɓen shugabanni bisa ra’ayinsu, tare da tabbatar da zaman lafiya.
Muƙaddashin Daraktan NOA na Jihar Kano, Malam Nura Liman, ya ce hukumar za ta kai shirye-shiryen wayar da kan jama’a zuwa ƙananan hukumomi 44 na jihar, tare da haɗin gwiwar sarakunan gargajiya.
A nasa jawabin, Sarkin Rano, Ambasada Muhammad Isa Umaru, ya tabbatar da goyon bayan masarautarsa ga ƙoƙarin hukumar na samar da zaɓe cikin lumana.
