
Aminu Abdullahi Ibrahim
An samu rikici tsakanin Sojojin dake gadin kamfanin shinkafa na Fortune Rice Mills Limited dake Sharada da hukumar tabbatar da bin dokokin muhalli ta kasa (Nesrea).
Da tsakar ranar Litinin dinnan ne ma’aikatar hukumar dake tabbatar da bin dokokin muhalli ta kasa Nesrea suka je kamfanin shinkafa na Fortune Rice Mills Limited dake rukunin kamfanoni na Sharada domin rufewa.
Sojojin sun kashe ’yan ta’adda huɗu tare da ƙwato makamai da kayan aiki a dajin Sambisa
Hukumar taje kamfanin ne tare da rakiyar jami’an ‘yan sanda biyo bayan zargin da akewa kamfanin na saba dokokin muhalli.

Sai dai zuwan su ke da wuya sai sojojin dake gadin kamfanin suka ce ba zata sabu na bindiga a ruwa inda suka yi kememe su kace ba za a rufe kamfanin ba.
Yayin hargitsin sojojin sun ce babu wanda ya isa ya rufe kamfanin matukar suna nan.
A cewarsu dole ne a sanar dasu kafin wata hukuma taje ko ta yi sumame a kamfanin na Fortune Rice Mills Limited.
Sai dai suma ma’aikatan hukumar ta Nesrea sunyi turjiya cewa sai sun rufe kamfanin inda suka umarci motocin dake lodin kaya su fice.
Bayan rufe kamfanin babban daraktan Nesrea shiyar arewa maso yamma Dakta Abdulraheem Mudashir, ya ce sun rufe kamfanin Fortune Rice Mills Limited sakamakon karya dokokin muhalli.
Ya ce kafin zuwansu sai da suka aikewa da kamfanin takardun gargadi amma basu gyara ba wanda hakan yasa suka dauki matakin kulle shi.
Rundunar sojin ƙasar nan ta tura sojoji 850 Jihar Filato.
Ya ce kamfanin baya kula da tsafatar muhalli kuma yana fitar da kura dake gurbata muhalli kuma hakan ya saba da sassa daban daban na dokokin hukumar.
Ya ce al’ummar yankin da wasu kamfanonin ne suka kai korafi kuma bayan hukumar (Nesrea) ta gudanar da bincike sai ta dauki mataki.
Dakta Abdulraheem Mudashir, ya ce duk wani guri ko kamfani da yaki kula da dokokin muhalli (Nesrea) zata dauki mataki akansa.
Ya ce zasu rubuta rahoto dangane da rufe kamfanin tare da turawa shalkwatar hukumar a matsakin kasa domin daukar mataki na gaba.
