Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyara a wani ɓangare na ƙarfafa alaƙa ga mamallakin tashar Premier Radio, Malam Abba Dabo, a gidansa da ke Kano.
Sanata Kwankwaso ya kai ziyarar ne domin ƙara dankon zumunci da kyautata alaƙa tsakaninsa da Malam Abba Dabo.
A yayin ziyarar, Kwankwaso ya samu rakiyar tsohon mataimakin Gwamnan Kano, Comrd Aminu Abdussalam Gwarzo tare da sauran mabiya da magoya bayansa.
