Mai alfarma sarkin musulmi
ya buƙaci al’ummar Musulmi da su fara duba jinjirin watan Zul-Hajji daga yau gobe Lahadi 17 ga watan Mayu 2026 wanda yayi daidai da 29 ga Zulƙida 1447 bayan Hijiriyya.
A wata sanarwar da Shugaban Kwamitin bayar da Shawara kan Harkokin Addinin Musulunci na majalisar Sarkin Musulmi kuma Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaid, ya fitar a Asabar din nan.
Sarkin Musulmi ya buƙaci duk wanda ya ga wata ya sanar da hakimi ko uban ƙasa na kusa da shi don sanar da Majalisar Sarkin Musulmi.
A cikin watan ne kuma Alhazai suke yin tsayuwar Tafa a ranar Tara ga wata, inda suke komawa su kwana a Filin Muzdalifa, sannan washegari ranar Babbar Sallah su yi jiran farko da yanka da aski da Ɗawafin Aikin Hajji.
