Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da nada Sarkin Gaya, Mai Martaba Alhaji Dr. Aliyu Ibrahim Abdulkadir, a matsayin Amirul Hajj na aikin Hajjin shekarar 2026.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa an nada Sarkin Karaye, Mai Martaba Alhaji Muhammad Muhammad Maharaz, a matsayin mataimakin Amirul Hajj.
Gwamnatin ta umurci Hukumar jin dadin Alhazai ta Kano da ta baiwa Amirul Hajj din da mataimakinsa cikakken goyon baya domin tabbatar da gudanar da ibadar cikin nasara.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Sanarwar na cewa, gwamnatin ta kuma yiwa tawagar Hajjin, shugabannin hukumar da ma’aikatanta fatan samun nasarar gudanar da aikin Hajjin bana, tare da addu’ar alhazai su gudanar da ibadarsu lafiya kuma su dawo gida cikin aminci.
