Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar Bichi Abubakar Kabir Abba Bichi, ya yabawa managartan ayyukan ci gaban da Shugaban kasa Bola Tinubu yake samarwa a arewacin Najeriya, tare da kalubalantar wadanda suke ganin Shugaban ya wofintar da yankin.
Abba Bichi ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wajen taron tabbatar da shi a matsayin dan takarar da zai wakilci karamar hukumar ta Bichi a zauren Majalisar tarayya.
Dan Majalisar ya ce ayyukan da gwamnatin tarayya karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu take samarwa a arewacin Najeriya a bayyane suke kuma ayyuka ne wadanda yankin zai ci gaba morar su nan da tarin shekaru masu zuwa.
Da yake jawabi, Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya yabawa Abba Bichi bisa irin ayyukan raya ƙasa da ya ke gudanarwa musamman a matakin ƙasa da kuma aiwatar da muhimman ayyukan mazabu da shirye-shiryen tallafawa al’umma.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito mai baiwa shugaba Tinubu shawara kan harkokin siyasa Kabiru Masari, wanda ya wakilci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, yana bayyana Abba Bichi a matsayin jajirtaccen shugaba mai nagarta wanda ke ba al’ummar mazabarsa wakilci mai inganci.
