Sanata Kabiru Marafa ya musanta labarin dake cewa shida tsowon gwamnan jihar Zamfara Abdul’aziz Yari sun sauya sheka daga APC zuwa jam’iyar PDP.
Sanata Kabiru Marafa ya musanta batun ne yayin tattaunawar sa da Tambarin Hausa a ranar Lahadi.
Ya ce abinda ya sani shine suna tattaunawa da wasu jam’iyu kan rashin adalcin da jam’iyar su ta APC tayi musu.
Ya ce sabon shugaban jam’iyar APC na kasa Abdullahi Adamu ya zauna da tsohon gwamna Abdul’aziz Yari sai dai ya ce duk da sun tattauna amma har yanzu basu cimma matsaya ba ta cigaba da kasancewa a cikin jam’iyar ko a kasin haka.
Sanata Kabiru Marafa ya ce idan har ba ayi musu adalci to tabbas zasu bar jam’iyar APC nan bada dadewa ba zuwa wata jam’iyar.
Ban wanke DCP Abba Kyari ba-Malami
Ya kuma ce magoya bayan su suyi watsi da duk wata sanarwa dake cewa sun bar jam’iyar ta APC a yanzu har sai anji daga bakin su tukunna.
A jiya Lahadi ne dai yayin taron manema labarai shugaban jam’iyar PDP na jihar ta Zamfara Kanar Bala Mande mai ritaya ya sanar da cewa Sanata Kabiru Marafa da Abdulaziz Yari sun koma jam’iyar PDP.