Saurari premier Radio
37.5 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAn sake hana Kano Pillars buga wasa a gida

An sake hana Kano Pillars buga wasa a gida

Date:

Hukumar dake shirya gasar Premier ta kasar nan (LMC) taci tarar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars naira miliyan tara tare da sauya mata inda zata rinka buga was anta na gida zuwa birnin tarayya Abuja.

Kano Pillars za ta dawo Kano da buga wasa
Hukumar ta dauki matakinne biyo bayan yadda wasu bata gari suka farwa ‘yan wasan Katsina United jim kadan bayan kammala wasan mako na 23 na gasar Firimiya ta kasar nan da suka fafata a Asabar din nan a filin wasa na Sani Abacha dake nan Kano.

 

Farmakin dai ya janyo lalacewar motar ‘yan wasan Katsina United tare da haddasa musu asara ta kayayyaki da dama.

Kano Pillars dai ta shafe fiye da shekara daya bata buga wasanni a gida inda kuma a yanzu aka sake dakatar da ita daga cigaba da fafafta wasannin nata a nan Kano a matsayin hukuncin abinda magoya bayanta sukayiwa kungiyar Katsina United.

Haka zalika hukumar ta kuma ce an ragewa sai masu gida maki uku inda tace za a kara ragewa matukar irin hyaka ta sake faruwa a nan gaba.
Sai dai kafin daukar matakin na LMC kungiyar Kano Pillars tayi allah wadarai da abinda ya faru.

Latest stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...

Related stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...