Saurari premier Radio
37.5 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKano Pillars za ta dawo Kano da buga wasa

Kano Pillars za ta dawo Kano da buga wasa

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Kamfanin shirya gasar league na kasa LMC ya baiwa kungiyar Kwallon kafa ta Kano Pillars damar dawowa Kano da wasanninta.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da sakataren hukumar Salisu Abubakar fitar ranar 12 ga Afrilu.

Ya ce hukumar ta yanke shawarar sahalewa Kano Pillars komawa gida bayan da ta karbi korafe-korafen jama’a da dama.

Kano Pillars dai ta shafe tsahon lokaci ba ta yi wasa a filin wasa na Sani Abacha ba.

Ta kuma koma Filin wasa na Ahmadu Bello dake Kuda kafin daga bisani ta koma Katsina filin Muhammadu Dikko.

A cewar hukumar ta LMC Filin wasa na Sani Abacha da ke nan Kano Bashi da nagartar da za a iya bugs wasa a cikinsa.

Yanzu haka dai Kano Pillars za ta kece raini da Katsina United a mako Mai zuwa da ake saran za ta buga wasan a filin na Sani Abacha

Latest stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...

Related stories