Saurari premier Radio
24.9 C
Kano
Thursday, April 11, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiHadarin Jirgin ruwa ya kashe mutum 29 a Sokoto

Hadarin Jirgin ruwa ya kashe mutum 29 a Sokoto

Date:

Hadarin jirgin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 29 a kauyen gidan magana da ke karamar hukumar Shagari a jihar Sokoto.

Jirgin ruwan dai ya rabe biyu ne a tsakiyar ruwan lokacin da suke tsaka da tafiya.

A cewar Kansilan mazabar, Bilyaminu Abubakar Ginga mutun 29, ne suka rasu cikin mutun 33.

Ya ce guda 23 mata ne yayin da shida daga ciki suka kasance maza.

“Jirgin yana daukar mutum 32 zuwa 33, matasa ne a cikinsa daga shekara 16 zuwa kasa, suna kan haya ne jirgin ya samu hadari a sanadiyar bugun icce da ya yi a cikin ruwan.

“[Jirgin] ya dauke su ne sufuri domin a kai su wasu kauyukka makwabta da karfe 10 na safen Laraba lamarin ya faru da su,” a cewarsa.

Ya bayyana cewa mutanen gari sun yi kokarin aikin gayya inda suka samu nasarar dauko gawa 29 ta matasan da ke cikin jirgin, an kuma ci gaba da neman ragowar.

Jirgin ruwan da ya yi hadari ya dauke su ne a hanyarsu ta zuwa daji domin samar da itacen girki da sauran wasu bukatu a wasu kauyukka na kusa da su.

A hanyarsu ta tafiya ce jirgin ya hadu da wani busasshen icen Giginya, abin da ya sanya ya rabu gida biyu matasan maza da mata suka nutse a tsakiyar ruwan.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories