Saurari premier Radio
26.4 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAtiku Abubakar: Zan mika mulki ga matasa da na gama wa'adina idan...

Atiku Abubakar: Zan mika mulki ga matasa da na gama wa’adina idan an zabe ni a matsayin shugaban kasa

Date:

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyar PDP Atiku Abubakar yayi alkawarin mika mulki ga matasa matukar aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Muhimman abubuwa 5 da zan mayar da hankali in na zama shugaban kasa: Atiku Abubakar

Cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun kungiyar yakin neman zaben sa Dr Victor Moses, ya fitar ya ce Atiku Abubakar ya bayyana hakane yayin taron da yayi da shugabanin kungiyoyin magoya bayansa guda dari biyu dake sassa daban daban na kasar nan a Abuja.

Atiku ya ce zayyi aiki tare da matasa tare da mika musu jagorancin kasar, yana mai cewa da yawan matasa suna bada gudunmawa a sha’anin siyasa a don haka zai tsaya musu.

Ya kuma bukaci matasan da su mara masa baya don ganin ya karbi mulkin kasar nan tare da alkawarin samar musu da damar maki masu yawa.

Ya ce abin takaici yadda matasa ke shan wahala karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya ce gwamnatin ta bar su a baya, yana mai cewa babu wata kasa da zatra cigaba ba tare da yin tafiya da matasa a sha’anin gudanar da mulki ba.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...