Saurari premier Radio
38.9 C
Kano
Friday, April 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMuhimman abubuwa 5 da zan mayar da hankali in na zama shugaban...

Muhimman abubuwa 5 da zan mayar da hankali in na zama shugaban kasa: Atiku Abubakar

Date:

Muhammad Bello Dabai

A larabar nan ce, tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji atiku Abubakar, ya bayyana kudirin tsayawa takarar shugabancin kasa a 2023, karkashin tutar jam’iyyar PDP.

Yayin taron, wanda aka gudanar a dakin taro na kasa da kasa dake babban birnin tarayya Abuja, Atiku yace ba komai ne ya sanya shi tsayawa takarar ba, illa burinsa na ceto Najeriya, wadda ta zamo tamkar jirgin ruwan dake nutsewa.

Yace zaben 2023, tamkar gadoji biyu ne dake kaiwa ga hadin kai da cigaba, ko kuma rabuwar kai da koma baya.

Atiku yace matukar aka zabe shi a matsayin shugaban kasa, gwamnatinsa zata maida hankali kan abubuwa biyar, wadanda suka kunshi hadin kan kasa, tsaro, tattalin arziki, ilimi, da kuma baiwa sauran matakan gwamnati ikon gudanarwa.

Yace “tun bayan yakin basasa, hadin kan Najeriya ya fada wani hali, kamar yadda yake a yanzu. Abin har ya kai ga yan Najeriya sun cire rai daga yuwuwar sake hade kansu.”

“Gwamnatin APC ta gaza kwarai wajen sauke nauyin dake wuyanta, musamman batun kare rayuka da dukiyoyin yan Najeriya. Mafi nuhimmancin yanci shine rayuwa, kuma itace tafi komai shiga wani hali a wannan gwamnati Dakarun sojinmu na fagen daga wajen yaki da bata gari, amma abin takaici babu kayan aiki.”

“Muna bukatar sabon shugabanci, wanda zai iya kaimu ga tudun mun tsira. A 2023, muna bukatar shugaban dake da masaniya akan hanyoyin gyaran Najeriya, mai fahimta da kyawun kalamai”.

Atiku ya kuma yi kira ga yan Najeriya da kada su bada kai bori ya hau wajen baiwa jam’iyya mai mulki damar raba kansu da addini ko kabila, ta yadda zasu manta da koma bayan da ta kawo musu.

“Suna so su dauke hankulanmu daga zarginsu kan lalacewar sha’anin tsaro da karuwar bakin talauci, mu dauki kanmu makiyan juna. Mu mayar da hankali kan matsalolinmu, ba banbancinmu ba, mu hade kai mu yaki rashin tsaro, talauci da rashin aikin yi.”

Abinda gwamnatina za ta maida hankali idan naci zabe

1. Hadin kai

“A iya tsawon rayuwa ta, ban taba yiwa yan Najeriya kallon wadanda kansu ke rabe ba, a idona duk daya ake. Bana iya banbance Bayerabe, Igbo, Bahaushe, ko Fulani, ko kuma dan Arewa da dan Kudu. Amma hadin kai baya yuwuwa face sai akwai daidaito da adalci, wannan tasa zanyi shugabanci bisa adalci da daidaito.”

2. Tsaro

“Me yasa tsaro ya zama wajibi? sabida shine alamar dake nuna cewa akwai gwamnati, idan aka rasa shi, to ba masu tada zaune tsaye zamu zarga ba, gwamnatin da ta bada kai bori ya hau ce abar zargi. In har kuka zabe ni, to ba zan zurawa matsalar tsaro ido ba, face sai nayi maganinta”

3.Tattalin arziki

“Tabbataccen tsaro shine ginshikin bunkasar tattalin arziki, kun ce mu koma gona, amma baku samar da tsaro a gobar ba.

Sannan a 2015, duk dala daya, daidai take da naira 197, amma a gwamnatin APC, darajar naira tayi karyewa mafi muni a tarihi, a yanzu da nake magana, ana canzar da dala daya akan sama da naira 400, farashin gwamnati.

Lokacin da APC ta karbi mulki, bashin da ake bin Najeriya kwata kwata Triliyan 12 ne, amma yanzu ya karu zuwa triliyan 32, kuma so suke su kara ciwo bashin wasu kudin. A gwamnati na, zan rage ciwo bashin gwamnati, domin barazana ce ga gobe kasa.

Zamu gudanar da tsarin tattalin arziki da zai baiwa kowa damar yin gaba, musamman kananan sana’o’i ta hanyar karbar harajin da bai taka kara ya karya ba.

Zamu fadada cigaban masana’antu masu zaman kansu, domin bunkasar tattalin arziki.”

3. Ilimi

“Ya zama wajibi duk dan Najeriya ya sami ilimi kyauta, akalla ko da zuwa matakin sakandare ne. Nasan muhimmancin ilimi, idan ba a sanadinsa ba, ta yaya mutum irina, wanda ya taso cikin rashin gata zai zama wani abu a Najeriya? Ba’a kwatanta nasarar ilimi ta fuskar yawan daliban dake aji ko makaranta ba, ana auna shi ne ta fuskar nagarta da kuma tasirin da zai iya yi. Wannan tasa zamu kalli bangaren ta hanyar bunkasa nagartarsa, da kuma baiwa kowa damar samunsa.”

4. Lafiya

“Bai dace dan Najeriya yayi fargabar kwanciyabrashin lafiya ba don bashi da kudin magani. Zamu yi abinda ya dace a bangaren domin duk wani dan Najeriya ya rabauta da kulawar da ta dace.

Atiku ya kuma yi tsokaci game da matsalar rashin man fetur a kasa, inda yace zasu samar da wadatattun matatun mai na cikin gida, ta yadda za’a ci gajiyar saukin farashinsa.

Sannan yasha alwashin dakile tsadar man ta hanyar sabon tsarin makamashi da zai samar.
Har ila yau, Atiku yace gwamnatinsa zata zuba kudi a bangaren wutar lantarki domin bunkasa ta ga yan Najeriya.

Kalubalen dake gaban Atiku

Mafi girman kalubalen da takarar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ke fuskanta itace, kiraue kirayen baiwa yan kudu takara a dukkanin jam’iyyu, ciki har da PDP.

An sha jiyo yadda gwamnonin yankin ke shirya tarukan hade kansu, domin yiwa duk jam’iyyar da taki amincewa da bukatarsu bore.

Har ila yau, a baya bayannan aka jiyo daya daga cikin kusoshin PDP dake burin tsayawa takarar shugaban kasar, Bukola Saraki, ya gana da masu ruwa da tsaki domin su hade kai wajen cimma nasarar takararsa.

To sai dai, Atiku, wanda jam’iyyar ta PDP ta baiwa tikitin takara a 2019, har yanzu yana da kwarin gwiwar cewa lokaci bai kure masa ba.

Waiwayen 2019

Atiku Abubakar, shine ya zamo zakaran gwajin dafin jam’iyyar PDP a 2019, wanda yasha kayi a hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC.

Ya sami kuri’u 11,262,978, yayinda abokin karawarsa, Muhammadu Buhari, ya sami kuri’u 15,191,847.

PDP ta kawo jihohi 18 cikin jimillar 36 da ake dasu a Najeriya, sannan APC mai mulki taci jihohi 18.

Galibin jihohin da PDP taci sun fito daga yankin kudu, kuma tazarar kuri’un da ta rika baiwa APC basa wuce 200,000, yayinda a Arewa, inda APC tafi samun kuri’u, an sami tazara har ta sama da miliyan 1.

A jihar Kano, wadda itace alkiblar siyasar Najeriya, APC ta sami kuri’u 1,464,768, inda PDP ta sami 391,593.

Mafi yawan kuri’un da PDP ta samu a dukkanin jihohin shine 649,612, wadanda suka fito daga jihar Kaduna, amma APC ce ta lashe jihar da kuri’u 993,445.

Latest stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...

Related stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...