Saurari premier Radio
40.5 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAddiniTukuntawa Foundation: Marayu 300 sun amfana da tallafi

Tukuntawa Foundation: Marayu 300 sun amfana da tallafi

Date:

Gidauniyar tallafawa marayu da marasa karfi ta unguwar Tukuntawa (Tukuntawa Foundation) ta raba abinci da kayan sawa ga marayu guda 300 dake unguwar.

Kwalejin fasaha ta Kano ta kara wadin rijistar dalibai na bana
Premier Radio ta ruwaito cewa an gudanar da rabon tallafin ne a Lahadin nan a makarantar Firamare dake unguwar ta Tukuntawa.


Gidauniyar wacce ke cika shekaru biyu da kafuwa ta kuma dauki nauyin marayu guda hamsin don yin karatu a makarantu masu zaman kansu daban daban dake cikin unguwar.

Da yake jawabi a wajen taron shugaban gidauniyar Malam Yakubu Abubakar, ya ce sun tallafawa marayun ne da abinci da kayan sawa domin suyi bikin sallah daidai da ‘ya’yan da iyayen su suke a raye.


Ya ce zasu tabbatar da cewa yaran da suka dauki nauyin karatun su na zuwa makarantun da aka turasu.

Ya kara da cewa an samu karin wadanda suka amfana da tallafin idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata wacce suka rabawa marayu 240 tallafi.

Abubakar Yakubu, ya kuma yi alkawarin ribanya tallafin da suke bayarwa a shekaru masu zuwa duba da yadda mawada dake ciki da wajen unguwar ke bada gudunmawar su.


A nasa bangaren mai unguwar Tukuntawa Alhaji Nuhu Garba Musa, ya yabawa gidauniyar tare da yin kira ga sauran mawadata wajen ganin sun bada tasu gudunmawar.

Mai unguwar ya kuma ce shugabancin sa zai hadakai da gidauniyar don aiwatar da tsaren tsaren ta don cigaba da tallafawa mabukata.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...