Saurari premier Radio
32.9 C
Kano
Friday, April 26, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiIngila zata hana 'yan wasan kwallon kafa yin tallan Caca (Gambling)

Ingila zata hana ‘yan wasan kwallon kafa yin tallan Caca (Gambling)

Date:

 

Hukumar dake kula da tallace tallace ta kasar Burtaniya ta sanar da samar da tsauraran dokoki akan tallace tallacen caca don kare yara kanana da masu kallon wasanni.

Dokokin zasu shafi kamfanonin dake amfani da ‘yan wasan kwallon kafa da sanannun mutane wajen tallata caca don kare yara yan kasa da shekaru 18.

Shugaban hukumar Shahriar Coupal, ya ce dokokin dai sun sha banban da dokokin tallar caca da ake dasu inda wadannan zasu hana amfani da hoto da sauran abubuwan daka iyayin tasiri akan yara.

Cikin dokokin dai akwai hana manyan ‘yan kwallo da suka shahara ga yara ‘yan kasa da shekara 18 yin tallan caca a kafafen sada zumunta.

Haka zalika dole ne ayi amfani da madogara dake nuna cewa ba zasuyi tasiri akan yara ba sannan manyan jaruman fina finai suma ba zasu rinka tallata cacar ba.

Sai dai hukumar tace dokokin zasu fara aiki ne daga ranar daya ga watan Oktoba na shekarar da muke ciki.

A watan Oktoba na shekarar 2020 ne hukumar ta fara tuntubar masana kan tasirin kasuwanci da tallace tallacen caca akan kananan yara da matasa da kuma manya da zasu iya cutuwa.

Wahalar tallafin mai za ta kare ne a kan ’yan Najeriya —Gwamnati

Inda hukumar tace samar da dokokin zai taimaka wajen kare yaran daga hatsarin da yin tallan ke dashi.

Latest stories

Related stories