24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiWahalar tallafin mai za ta kare ne a kan ’yan Najeriya —Gwamnati

Wahalar tallafin mai za ta kare ne a kan ’yan Najeriya —Gwamnati

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Gwamnatin Tarayya ta ce ’yan Najeriya su shirya wa abin da zai biyo bayan matakin da gwamnatin ta dauka na jinkirta lokacin daina biyan tallafin man fetur.

Mai Magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ne bayyana hakan inda ya ce  jazaman ne ’yan Najeriya su shirya wa abin da zai biyo baya idan aka ci gaba da biyan kudin tallafin man bayan watan Yunin 2022.

Gwamnatin ta yi kashedin ne bayan Majalisar Zartarwa ta kasa ta amince a kashe Naira tiriliyan uku wajen biyan tallafin man a shekarar 2022 da muke ciki.

Hakan na nufin za a samu kari a kasafin 2022 na Naira tiriliyan 17.1 da gwamnatin ta yi wanda aka yi ta surutai a kai saboda yawansa da kuma yawan basukan da gwamnatin za ta ciyo domin aiwatar da shi.

Sai dai kuma Femi Adesina ya yi watsi da zargin da jam’iyyar adawa ta PDP ta yi cewa gwamnatin za ta ci gaba da biyan tallafin ne domin ta fake ta shi wajen tara kudaden yakin neman zaben jam’iyyar APC mai mulki a 2023.

Latest stories