Saurari premier Radio
37.9 C
Kano
Friday, April 26, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAddiniHisba ta fara kamen shisha a Kano

Hisba ta fara kamen shisha a Kano

Date:

Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta kai sumame shagunan da ake sayar da shisha a kan titin Bompai da ke  nan Kano a jiya Laraba, inda ta kama dillalan shishar, domin tabbatar da dokar hana sha da siyar da ita a Kano.

Premier Radio ta ruwaito wannan dai shi ne karo na farko da gwamnati ta fara aiwatar da dokar, tun bayan da majalisar dokoki ta sanyawa ƙudurin dokar hannu.

Sashi na 13(7) na dokar shisha, wacce a ka sanyawa hannu a ranar 15 ga watan Nuwamba, 2021, ya ce sha da ta’ammali da shisha haramun ne a Jihar Kano.

Tuni dai hukumar ta fara kama masu sayar da shishar inda su ma su ka ce duk da an hana, har yanzu ana kawo musu ita da ga kasashen Dubai da China.

Haka kuma sun yi ƙorafin cewa an fara aiwatar da dokar ne ba tare da an basu wa’adi ba.

Sun kuma ƙara da cewa ya kamata a ce an wayar musu da kai da kuma sanarwa mai tsawo kafin a zo a fara kai musu farmaki a wajajen sana’ar su.

Sun ce su sun za ci dokar ta tsaya ne a wajen masu guraren shan shishar ba wai dillalin ta ba.

Da ya ke ganawa da manema labarai, Shugaban Hukumar Hisbah, Muhammad Harun Ibn-Sina, ya ce sun fara sumamen ne domin haka ayyukan hukumar ya gada.

A cewar sa, sashe na 13(7) na dokar hana shisha ya tabbatar da cewa ta an haramta amfani da ita a jihar Kano, inda ya jadda ƙudurin hukumar Hisbah na ci gaba da hana sha da sayar da ita a faɗin jihar.

Ya kuma jaddada ƙudurin hukumar wajen yaƙi da baɗala da kuma umarni da kyawawan ayyuka a jihar.

Latest stories

Related stories