Saurari premier Radio
26.4 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBuhari Ya aza harsashin ginin masana’antar simintin BUA a Sakkwato

Buhari Ya aza harsashin ginin masana’antar simintin BUA a Sakkwato

Date:

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aza harsashin aikin gina masana’antar siminti ta kamfanin BUA a Jihar Sakkwato.

Buhari ya kaddamar da aikin gina masana’aantar wadda za ta samar da tan miliyan uku na siminti a shekarane ne a yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa ziyarar aiki a Jihar Zamfara.

Buhari, wanda Gwamnan Jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya karbi bakuncinsa, ya samu rakiyar Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefele, Shugaban Rukunin Kamfanin BUA, Alhaji AbdulSamad Rabi”u da kuma Shugaban Kamfanin Jiragen Sama na Max Air, Alhaji Dahiru Bara’u Mangal da sauran manyan mutane.

Tun kafin ziyarar shugaban kasar aka tsaurara matakan tsaro a birnin Sakkwato, gami da taikaita zirga-zirgar ababen hawa a hanyar zuwa masana’antar da Buhari zai kafa harsashin gininsa.

A shekarar 2020 ne Shugaban Kamfanin BUA ya yi alkawarin gina karin masana’antun siminti uku a jihohin Sakkwato da Adamawa da kuma Edo domin kara karfin kamfanin na samar da siminti daga metric ton miliyan 11 zuwa metric ton miliyan 20.

Buhari a Zamfara

Ziyarar Buharin ta ranar Alhamis na zuwa ne bayan sojoji sun tsaurara wajen yi wa ’yan bindiga luguden wuta a jihar, suka kuma karya lagonsu.

Hare-haren sun sa maharan watsuwa zuwa wasu sassa na Jihar Sakkwato, musamman yankin kananan hukumomin Sabon Birni da Isa, inda suka rika yi wa mutane kisan gilla.

Idan ba a manta ba, a kwanakin bayan ’yan bindiga sun tare wata motar fasinja a Sabon Birni inda suka kashe mutum sama da 20 ta hanyar cinna musu wuta a cikin motar.

Kashe-kashen Sakkwato, musamman na Sabon Birni sun haifar da zanga-zanga, saboda a lokacin an zargi Buhari da halartar taron kaddamar da littafin tarihin wani jigo a jam’iyyar APC, Cif Bisi Akande, a Legas, a daidai lokacin da aka yi wa fasinjojin kisan gilla.

Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa kaddamar da wasu jiragen yaki da unduanr Sojin Ruwan Najeriya ta kera ne ya kai shi Legas, ba wai musamman domin halartar kaddamar da littafin ba.

Buhari ya kuma tura tawaga ta musamman wadda ta kunshi manyan hafsoshin tsaro domin yin ta’aziyya da kuma daukar matakan kakkabe ayyukan ’yan bindiga.

A kwanakin baya ba hukumomi a Jihar Zamfara sun ce maharan suna neman a yi sulhu da su domin su daina aika ta’addancinsu.

Idan ba a manta ba a kokarin murkushe ’yan bindiga, a baya gwamnati ta rufe layukan sadarwa a sassan jihohin Jihar Zamfara da Katsina da Neja da Kaduna.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...