Saurari premier Radio
40.5 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiHadarin shalkwaftan 'yan sanda ya jikkata mutane shida a Bauchi

Hadarin shalkwaftan ‘yan sanda ya jikkata mutane shida a Bauchi

Date:

Mutum shida ne suka ji mummunan rauni a hatsarin da wani helikwafta mallakin rundunar ƴan sandan Najeriya ya yi a Bauchi a jiya Laraba.

Gidan rediyon gwamnatin tarayya ya ruwaito Hukumar Bincike Haɗurra ta ƙasar, AIB tana tabbatar da labarain.

Sai dai a sanarwar da hukumar AIB ta fitar ɗin ta ce babu wanda ya mutu a hatsarin.

Hukumar ta ce Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Najeriya NAMA ce ta sanar da ita faruwar lamarin kuma tuni an fara bincike.

Hukumar ta nemi duk wanda lamarin ya faru a kan idonsa ko ya naɗi wani bayani na faruwarsa da ya kai mata don taimaka wa wajen binciken da ake yi.

AIB ta kuma buƙci jama’a da ƴan jarida da su tsare sirrin waɗanda hatsarin ya rutsa da su ta hanyar dakatar da yaɗa jita-jita kan abin da ya haddasa hatsarin har sai an fitar da bayani a hukumance.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...