Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Wednesday, April 24, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKasuwanciHukumomin Dubai sun dage haramcin da suka sanya wa wasu jiragen Afirka

Hukumomin Dubai sun dage haramcin da suka sanya wa wasu jiragen Afirka

Date:

Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta sanar cewa za ta dage dakatarwar da ta yi wa dukkanin jiragen sama na fasinja, da ke zuwa kasar kai tsaye da kuma masu yada zango daga wasu kasashen Afirka 12, tun daga ranar Asabar 29 ga watan Janairu.

Hukumomin sun bayyana wannan mataki ne kusan sa’a 48 da Kenya ta janye irin wannan haramci na shigar dukkanin jiragen sama na fasinja daga Daular zuwa kasar ta gabashin Afirka.

Gwamnatin Kenya ta sanya dokar ne a kan jiragen da ke zuwa kasarta daga UAE, ranar 10 ga watan Janairu a matsayin martini ga irin wannan haramci da hukumomin Daular Larabawan suka sanya wa jiragen fasinja daga Kenya a watan Disamba da ya wuce.

Yanzu wannan dage haramcin shigar da Hadaddiyar Daular Larabawan za ta yi ya shafi fasinjoji daga

Kenya da Tanzania da Ethiopia da Najeriya da Jamhuriyar Kongo da Afirka ta Kudu da Botswana da Eswatini da Lesotho da Mozambique da Namibia da kuma Zimbabwe.

Sai dai kuma za a bukaci kowane fasinja ya yi gwajin korona uku kafin a bar shi ya shiga kasar.

Zai gwajin farko sa’a 48 kafin ya tashi, sannan na biyu a lokacin da zai tashi a filin jirgi, kana kuma a yi masa gwaji na uku idan ya sauka a Daular, kuma dole ne dukkanin gwajin ya kasance mutum ba ya dauke da cutar.

A wani sakon tuwita da hukumomin kasar Laraban suka fitar sun ce za su fitar da dokokin da za su sanya wa fasinjoji daga Uganda da Ghana da kuma Rwanda.

Hukumomin kula da sufurin jirgin saman fasinja na Dubai sun nuna damuwa kan yadda ake samun wasu fasinjoji daga Kenya da ke dauke da shedar cewa ba sa dauke da cutar korona, amma kuma idan aka yi musu gwaji a kasashen Gabas ta Tsakiya, sai a ga suna dauke da ita.

Latest stories

Related stories