Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiGwamnatin tarayya za ta sake bibiyar lasisin masu hakar ma'adana

Gwamnatin tarayya za ta sake bibiyar lasisin masu hakar ma’adana

Date:

Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin ta na sake bibiyar lasisin masu hakar ma’adinai a kasar nan, domin sake tabbatar a inganta bangaren dama kawo masu ayyukan masu hakar madinan ba bisa ka’ida ba.

Ministan albarkatun kasa, Dr Dele Alake ne ya bayyana hakan a jiya Alhamis, ya yin taron masu ruwa da tsaki a bangaren zuba jari, wanda ya gudana a shelkwatar ma’aikatar dake birnin tarayya Abuja.

Dr Dele ya kara da cewa gwamnatin tarayya a shirye take don daukar matakin ba sani ba sabo, kan duk kamfani hakar ma’adinan da bai samar da yanayin cikakkiyar kariya ba ga ma’aikatansa.

Hakan wasu dai na ganin cewa akwai yiwuwar wasu daga cikin kamfanonin su iya rasa lasisin su, musamman ganin yadda gwamnatin ta bayar da himma wajen ganin an samar da yanayin aiki mai nutsuwa da zai taimaka wajen rage salwantar rayuwan ma’aikatan da kan hako ma’adinan.

Ministan ya kuma kara da cewa gwamnati ta bujiro da shirin sake bibiyar lasisin masu hakar ma’adinan ne domin sake bayar da dama ga masu son zuba jari, musamman kamfanonin dake da sha’awa.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...