Wasu iyayen matasa masu shirin fara bautar ƙasa ta NYSC daga Jihar Oyo sun shiga cikin tashin hankali, bayan masu garkuwa da mutanen da suka sace ’ya’yansu sun ba su wa’adin sa’o’i 24 da su biya kuɗin fansa naira biliyan ɗaya domin sakin waɗanda aka sace.
Iyayen sun bayyana hakan ne yayin wata ganawa da Sarkin Ibadan, Oba Rashidi Ladoja, a gidansa da ke unguwar Bodija a Ibadan, inda kwamishinan ’yan sandan jihar da wasu shugabannin gargajiya suka halarta. Sun ce masu garkuwar na tuntubarsu ta wayoyin waɗanda aka sace, suna neman naira miliyan 50 kan kowane mutum.
Rahotanni sun ce an sace matasan ne a ranar Alhamis, yayin da suke tafiya daga Ibadan zuwa sansanonin horas da ’yan bautar ƙasa da ke jihohin Abia da Akwa Ibom. ’Yan bindigar sun tare motocin bas guda biyu da ke ɗauke da su a yankin Umunoha, da ke kan hanyar Owerri zuwa Onitsha a Jihar Imo, inda suka yi awon gaba da fasinjojin zuwa cikin daji.
Sai dai akwai rahotanni masu saɓani kan adadin waɗanda aka sace. Yayin da wasu iyaye suka ce mutum 20 ne abin ya shafa, rahotannin farko daga kamfanin motocin da wasu kafafen yaɗa labarai sun nuna cewa mutum 19 aka yi garkuwa da su. Haka kuma, rundunar ’yan sandan Imo ta sanar da ceto mutum 10, amma ba ta tabbatar ko suna cikin waɗanda aka sace daga motocin ba.
Iyayen sun roƙi gwamnatin tarayya da ta jihohin Oyo da Imo, da hukumomin tsaro, da su gaggauta shiga tsakani domin kuɓutar da ’ya’yansu cikin ƙoshin lafiya. Sun bayyana damuwarsu kan yadda za su iya biyan kuɗin fansar da ake nema, musamman ganin cewa wasu daga cikinsu ba su da halin kuɗi.
A halin yanzu, rundunar ’yan sanda ta ce jami’an tsaro na gudanar da aikin haɗin gwiwa domin gano inda masu garkuwar suke da kuma kuɓutar da sauran waɗanda aka sace. Gwamnatin Oyo ma ta yi Allah-wadai da lamarin tare da tabbatar wa iyayen cewa tana aiki da hukumomin da abin ya shafa domin ganin an kuɓutar da matasan.
