Tawagar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, mai ɗauke da magoya bayansa sama da dubu 10, ta isa jihar Kaduna domin halartar taron ƙaddamar da takarar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a zaɓen 2027 wanda za a gudanar a yau Asabar.
Tawagar ta ƙunshi mukarraban gwamnati, ’yan siyasa, jami’an tsaro, masu amfani da kafafen sada zumunta da kuma manema labarai daban-daban.
Ana sa ran Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai ƙaddamar da takararsa a hukumance yayin taron da misalin karfe 2 na rana, wanda hakan ke cikin shirye-shiryen jam’iyyar APC na tunkarar zaɓen shugaban ƙasa da sauran muƙaman siyasa na shekarar 2027.
Tuni jihar ta Kaduna tayi cikar kwari da magoya daga sassa daban daban na Najeriya.
Wakilinmu, Kamal Umar Kurna, ya rawaito cewa halartar Gwamna Abba Kabir Yusuf da magoya bayansa na daga cikin matakan nuna goyon bayan Kano ga takarar Shugaba Tinubu, tare da bayyana aniyar jihar na bayar da gagarumar gudummawar ƙuri’u a zaɓe mai zuwa.
