Ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Injiniya Seyi Makinde ta soki shirin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027 a jihar Kaduna.
Ƙungiyar, mai goyon bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APM, ta ce gudanar da gangamin a Kaduna ba zai magance matsalolin tsaro da tattalin arziki da take zargin gwamnatin Tinubu ta gaza shawo kansu ba.
A cikin wata sanarwa da daraktan sadarwar ƙungiyar, Richard Nnanna Ihediwa, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta yi zargin cewa manufofin gwamnatin tarayya sun jefa ’yan Najeriya da dama cikin mawuyacin hali.
Ta kuma tambayi irin ci gaban da Arewa maso Yamma ta samu a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, musamman ta fuskar tsaro, tsadar rayuwa da ci gaban al’umma.
Ƙungiyar ta tuno da alkawarin da Shugaba Tinubu ya bayar a wani gangamin APC a Kaduna ranar 13 ga Disamba, 2022, na kawo ƙarshen ayyukan ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da masu kisan kai a yankin.
Sai dai ta ce har yanzu ana ci gaba da samun kashe-kashe, garkuwa da mutane da tilasta wa jama’a barin muhallansu a wasu sassan ƙasar, duk da shafe sama da shekaru uku da fara mulkinsa.
