Gwamnatin Tarayya ta umarci hukumomin tsaro, cibiyoyin lafiya da sauran hukumomin da abin ya shafa da su ƙara tsaurara sa ido kan matafiya da ke shigowa Najeriya, domin hana yaɗuwar cutar Ebola.
Wannan mataki na zuwa ne bayan gwamnatin ta nuna damuwa kan rahotannin yiwuwar karya ƙa’idojin tantance matafiya da aka tanada domin dakile shigar cutar cikin ƙasar.
A cikin wata takarda mai kwanan wata 22 ga Oktoba, 2026, Ma’aikatar Lafiya da Walwalar Jama’a ta Tarayya ta ce umarnin ya biyo bayan gargaɗin ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaron Ƙasa, game da yiwuwar rashin bin ƙa’idojin shiga ƙasar.
Ma’aikatar ta buƙaci hukumomin da abin ya shafa su riƙa tattara bayanai tare da kai rahoton duk wani yunƙuri ko lamari da ya shafi karya ƙa’idojin kariya.
Ta kuma jaddada wajabcin bin ƙa’idojin tare da hana duk wani katsalandan ga jami’an da ke gudanar da aikin tantancewa da sauran matakan kariya.
