Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wani manomi mai shekaru 71, Bamidele Mathew, wanda aka fi sani da Dele Photo, tare da ɗansa mai shekaru 18 a garin Odo-Owa da ke ƙaramar hukumar Oke-Ero ta jihar Kwara.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata, a kan hanyar Idofin-Igbana, yayin da manomin da ’ya’yansa suke kan hanyarsu ta zuwa gona.
Wani ɗan manomin da ya tsallake harin ya ce maharan sun fito daga cikin daji, suka yi musu barazana da bindigu, sannan suka yi awon gaba da mahaifinsa da ƙanensa.
Wata surukar manomin ta bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalinsa, inda suka buƙaci kuɗin fansa naira miliyan 20 domin sakin waɗanda aka sace.
Ta yi kira ga gwamnatin jihar Kwara da masu hannu da shuni da su taimaka wajen ganin an kuɓutar da mutanen biyu cikin ƙoshin lafiya.
