Rundunar ’yan sandan Najeriya ta sanar da kama wasu mutane da ake zargi da hannu a damfarar intanet, yaudarar soyayya, damfarar zuba jari da kuma halatta kuɗaɗen haram.
Mataimakin Sufeto Janar na ’yan sanda mai kula da Cibiyar Yaƙi da Laifukan Intanet ta Ƙasa, Akaniyene Ezima, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja.
Ya ce binciken da rundunar ta gudanar ya shafi laifuka daban-daban da ake zargin sun jawo asarar makudan kuɗaɗe ga mutane a ƙasashen Amurka, Birtaniya, Kanada da Ostiraliya.
A wani ɓangare na binciken, jami’an ’yan sanda sun kama wasu mutum huɗu a garuruwan Agbor da Okpanam na jihar Delta, bayan samun bayanan sirri daga Hukumar Yaƙi da Laifukan Ƙasa ta Birtaniya.
Ana zargin waɗanda aka kama da amfani da sunayen bogi a kafafen sada zumunta wajen yaudarar mutane su zuba kuɗaɗensu a shafukan yanar gizo na bogi.
Binciken farko ya nuna cewa ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ya yi amfani da kuɗaɗen dijital, ciki har da cryptocurrency, wajen karɓa da tura kuɗaɗen waɗanda aka damfara.
Rundunar ta ce ta gano kadarorin cryptocurrency da darajarsu ta kai dala dubu 15 da ɗari tara, waɗanda aka ajiye a wani asusu.
Haka kuma, rundunar ta ce ta kama wasu mutum biyu a jihar Delta bisa zargin hannu a wata damfarar soyayya da ta shafi wasu tsofaffi mazauna Kanada tsakanin shekarun 2020 zuwa 2024.
