Ma’aikatar kasuwanci ta Kano ta rantsar da sabon kwamitin riƙo na kasuwar Ƴankaba
Ma’aikatar Zuba Jari, Kasuwanci, Masana’antu da Haɗa-haɗar Kasuwanci ta jihar Kano ta rantsar da sabon kwamitin riƙo na ƙungiyar masu sayar da kayan marmari da kayan lambu na kasuwar Ƴankaba da ke Kano.
Da yake jawabi yayin bikin rantsarwar, Daraktan Kasuwanci na ma’aikatar, Alhaji Abubakar Bello Gwarzo, ya buƙaci sabbin shugabannin da su ɗauki shugabanci a matsayin amana da za a tambaye a gaban su Allah.
Ya kuma ƙarfafa musu gwiwa da su riƙa tafiya da dukkan mambobin ƙungiyar tare da gudanar da ayyukansu bisa kundin tsarin mulki da dokokin ƙungiyar.
Haka kuma ya yi kira ga kwamitin amintattu da tsoffin shugabannin ƙungiyar da su bai wa sabon kwamitin haɗin kai domin gudanar da aikinta cikin nasara.
Kwamitin zai yi aiki na tsawon watanni uku kafin gudanar da sahihin zaɓe.
A nasa jawabin, shugaban kwamitin riƙon, Alhaji Hamisu Abdullahi, ya gode wa ma’aikatar da kuma mambobin ƙungiyar bisa amincewar da suka nuna masa da sauran mambobin kwamitin.
Shi ma shugaban kwamitin amintattu na ƙungiyar, Alhaji Danlami Umar, ya bayyana kafa kwamitin a matsayin mataki mai kyau wajen dawo da daidaito da ci gaban ƙungiyar.
Ya ƙara da cewa duk da cewa ƙananan hukumomi ne ke da ikon mallakar kasuwannin, kula da tafiyar harkokin kasuwanci yana ƙarƙashin ma’aikatar Zuba Jari, Kasuwanci, Masana’antu da Haɗa-haɗar Kasuwanci.
Sabon kwamitin riƙon mai mambobi tara ya haɗa da:
Alhaji Hamisu Abdullahi — Shugaba
Abdulrazaq Dankano — Mataimakin Shugaba
Umar Aminu — Sakatare
Aminu Ahmad Together — Mai Binciken Kuɗi
Aminu Inuwa — Jami’in Hulɗa da Jama’a
Idris Shuaibu Kafce — Sakataren Tsare-tsare
Abubakar Muhammad Kono — Ma’aji
Aminu Haruna — Jami’in Jin Daɗi
Ibrahim Ahmad Gatusu — Sakataren Kuɗi
